RIKICIN ZABEN MUSAWA: ABIN DA NAJI NA GANI

0

RIKICIN ZABEN MUSAWA:
ABIN DA NAJI NA GANI…
Alhaji Ali Maikano
@ katsina city news
Suna Ali Maikano, a bin da ya faru, ina cikin yantakarar da suka yi takara.a kujerar majalisar tarayya .musawa da Matazu.abin ya faru 27/5/2022 aka sa ranar zaben mu. To, tun wajen karfe 8:00 na safe, muna filin zabe, muka zauna shiru – shiru bamu ga kowa ba, har wajen karfe 3 da wani abu zuwa 4:00 na yamma, sai muka yi shawara, ni da sauran yantakar guda biyu, don mu duka ukun Muna wurin, guda daya baya nan shi ne, Abdullahi Ali, shi ba ya wajen . Sai muka ce shin, mu har yanzu bamu ga kowa ba, bamu ga Malaman zabe ba, sai muka ce mu je party office mu duba, mu ji ko shi Chairman zai mana wani bayani, muka taka muka je, can ma ba kowa. Muka ce to, wannan election ko an fasa shi ne, amma dai akwai Yansanda, saboda da safe,an dan samu yamutsi a wurin.

To, muka samu jinkiri a wurin da ba a bar mu, muka shiga ba, amma sai suka bar mu muka shiga, muka ce Chairman muka zo gani aka ce “bayanan” don haka ba wani bayani, amma a waje akwai matasa da yawa, yawancinsu duk da makamai a hannunsu, domin akwai wanda na gani da wata bakar bindiga a hannun shi. Har na ce taron nan na mene ne? Aka ce magoya bayan wani Dan takara ne , suka zo.

Da har na tsaya ina cewa don Allah a yi hakuri a daina tashin hankali, don kar ai fitina, sai aka zo aka ce man, na bar nan don kar su yi maka lahani, shi ke nan sai muka bar nan muka koma can wurin zabe.

Sai muka ga ana ‘yan guje-guje haka, ana jefa teargas, Yansanda suna jefa teargas yara na guje-guje. Sai muka yi shawarar gara mu tashi mu bar wurin nan, sai muka tafi, can gidan, dayan Dan takarar Wanda ake cema Mamuda Maizamani, gidan shi ba nisa sai muka tafi gidan shi, da ni da shi da D Murtala, bamu taba haka ba, sai ranar, muka je muka zauna, muka ce ya wannan abu haka. Ni ban san komai ke faruwa ba? aka ce tun dazu ake wannan fitina, ni hankalina bai kai wurin ba, na ce in dai ana wannan fitina haka ya za ai a yi zabe?

Sai can wajen mintuna talatin aka zo aka ce an fasa ma wani yaro kai, to, an tafi da shi asibiti, sai ga wani ya zo ya ce ” an kashe mutum daya” can ma wani ya zo ya ce ” an kashe mutum daya” mutum biyu ke nan. Na ce kun ga wannan wurin ba wurin zama bane tunda ba nisa zuwa wurin, mu bar wurin nan don kar su zo su shigo mana, suka ce a’a ba komai.

Muna nan zaune, sai muka ji wai an ce an yi zabe, an fitar da winner, a’a mu da agent dinmu da observers dinmu duk muna wuri Daya, ba wanda ya je wurin zabe.

Mun ji an ce an kashe mutum, ga mutane an kawo mana hotuna, ga wasu an kai su asibiti, aka ce an gama zabe? Na ce ni dai gaskiya ba zan zauna wurin nan ba, karshe tun da an gama zabe.su yo kanmu, sai na shiga mota ta na dawo Katsina.

Wannan shine abun da na sani. da daddare na je na samu mai girma Gwamna na gaya ma shi, to, ga abin da ya ke faru, ya ce to, wannan abu, sai dai mu rubuto, petition, muka rubuta mu ka kai. To, abin da muka yi ke nan.

Ali Maikano: Ni dai na san ba ai man zabe ba, in aka ce an man, ba ai mana adalci ba, don inda muke ma ba nisa, dan lokacin da za ai abin da an aiko ku taho za ai zabe, ba wanda aka aiko, to, amma rikicin dake wurin dole mu tashi.
Yanzu mun rubuta koke muna neman ayi mana adalci. Kuma muna sauraren su.
Yanzu haka na dawo Kaduna wajen sana o ina ina jiran irin adalcin da )za ayi mana.
Muazu hassan
Bashir Suleman
Suleman Umar
katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here