DIKKO RADDA KA DAUKI AMINU WAZIRI….lnji Gammayar kungiyoyin matasa.
@ Taron Manema labarai
Mu ‘yan Kungiyar Gamayyar Kungiyoyin Matasa Jihar Katsina. (Coalition Of Katsina State Youths Groups), karkashin jagorancin Bashir Mamman Sabi’u Daura, mun hadu ne a nan domin kira ga sabon dan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar, Dr. Dikko Umar Radda, wanda yake shi ma yana cikin matasa a wata kidddigar ta duniya.
Da farko, muna tabbatar masa da duk goyon baya, da kuma tabbatar masa za mu ba shi duk hadin kai wajen cimma nasarar har zuwa gidan gwamnati. In kuma Allah ya kai shi za mu ba shi goyon baya ya samu nasara ga duk ayyukan alherin da yake fata da kuduri ga Jihar Katsina.
Na biyu. Muna kira ga al’ummar Jihar Katsina da su karanta sosai su kuma duba tsakanin ‘yan takarkarin da jam’iyyun Katsina suka fitar, musamam PDP da NNPP, za su ga cewa ba dan takarar da ya kai na APC, Dakta Umar Radda
Na uku. Muna kira ga Dakta Umar Radda da in zai zabi wanda zai masa mataimaki babu inda ya dace ya fito da mataimaki kamar garin Malumfashi, saboda muhimmancinta a siyasa, kasuwanci da kuma tasirin ta yankin Funtua.
Na hudu. A Malumfashi akwai wadanda suka dace da yawa, saboda Allah ya yi wa Karamar Hukumar baiwa da masu ilmi da arziki, amma wanda zai daidai da sabuwar tafiyar da za a shiga da sabbin tsare-tsare da za ka kawo na ciyar da Jihar Katsina gaba, shi ne Dakta Aminu Garba Waziri.
An haifi Dakta Aminu Waziri a garin Malumfashi a shekarar 1972. Ya yi karatunsa a ciki da wajen Nijeriya a kan ilmin Kidddigar Lissafin Gine-Gine, wanda ya fara daga Diploma ta kasa har ya kai digrin digirgir duk a fannoni daban-daban na Kimmiyyar Kidddigar Gine-Gine.
Ya halarci kwasa-kwasai daban-daban a ciki da wajen kasar nan. Yana cikin kungiyoyin kwarewa na fasahar gine-gine daban-daban a ciki da wajen kasar nan. Ya yi rubuce-rubuce daban-daban a kan ilminsa wadanda suka zama abin dogaro da kafa hujja.
Aminu Waziri ya yi aiki wurare daban-daban ciki har koyarwa da rike mukamai a manyan makarantun kasar nan, yanzu kuma shi ne Babban Sakatare a Ma’aikatar Gona ta Jihar Katsina.
A bangaren siyasa, Aminu Waziri dan jam’iyyar APC ne na gaskiya, ya rike Hukumar Ba Da Tallafin Gaggawa ta Jihar Katsina. Ya rike Shugaban Karamar Hukumar Malumfashi. Ya shiga kwamitoci daban-daban, wadanda duk ayyukan da ya yi na gani da fada ba boyayyu bane.
A sabuwar tafiyar da za a dora, wadda za ta habbaka ayyukan alheri na APC, irin Aminu Waziri shi ne daidai da zama mataimakinka.
Kana bukatar mataimaki mai ilmin zamani da na addini, wanda ya san darajar kowa.
Aminu Waziri shi ne Wazirin Doka na Mai Martaba Sarkin Katsina, kuma shi ne Turakin Malumfashi na Galadiman Katsina.
Muna fata wannan kira namu zai samu shiga.
Mun gode.
Sa hannu.
Bashir Mamman sabi u Daura
Hajia Hajara Abdullahi funtua
Cmrd sadiq Ibrahim katsina.