RIKICIN ZABEN MUSAWA: ABIN DA YA FARU A RANAR!!!

0

RIKICIN ZABEN MUSAWA:
ABIN DA YA FARU A RANAR!!!
……..inji Ibrahim D Murtala
@ katsina city news
Sunana Ibrahim D Murtala,Nine tsohon Dan majalisar musawa da Matazu daga 2015 zuwa 2019.A bin da ya faru a zaben fitar da Dan takarar a ranar 27/5/2022. Mun ga Gwamnan katsina mun fada ma shi abin da ya faru, dama mu masu takarar mu hudu ne.

Mu uku muna filin zaben tun safe har yamma ba abin da ya faru. Sai kawai muka ga an fara sarar mutane har an fara jikkata da jin cewa an kashe wasu , dama mu uku ne, da ni da Mamuda Lawal, sai Ali Maikano sai mu ka bar wajen .sai kawai muka ji wai har anyi zaben.kuma wai Ali Abdullahi ya chanye duk kuri un da aka jefa.105.

Bamu iya tsayawa,don sun kawo yandaba, na ji an ce daga Tsanyawa daga Bichi daga Shanono da wani gari ana ce masa Bulbulau, sai na ce bai kamata mu shiga zabe ba, don abin da zai faru damu ko magoya bayanmu, To, suka yi zabe su kadai, su ka ce Ali Abdullahi shi daya ya samu kuri’a 105 wato, duka kuri’un gaba daya.

Mu duka ukun muka zo da daddare muka samu Gwamna muka gaya ma shi, ya ce to, mu rubuta petition mu kai ma shi, ya hada mu da Appel commetee, mu ka rubuta, to, ka Ji abin da ya faru.

Katsina City News; KO AN KASHE WANI .?

D Murtala : Wanda da aka kashe mutum daya ne, kuma “cousins brother” di na ne, daga Matazu sunan shi Abdul Musa. Iyayen shi suna Kano, sun zo ne, su taya ni murna da hidimar zabe.

Katsina City News. Yaya aka kashe shi, sara ne ko bugu ne ko wani makami aka yi amfani da shi?

D .Murtala. To, wallahi ni ba zan ce ga yadda aka kashe shi ba, amma ina ga ma akwai saran daga baya kuma aka ce mota ce ta zo ta buge shi, daga nan aka dauke shi aka kai shi ko ina? Ko gidan Bala daga baya aka dauke shi aka kai shi asibiti. To, ni dai ban sa ni ba, don ba a wajen nake ba, don da ni da Ciroma da Mamuda Lawal duk muna can gidan Mamuda Lawal.abin ya faru.

Katsina City News: Wadanda aka ji ma ciwo, akwai wadanda ka sa ni?

D.Murtala. Kwarai da gaske akwai daya ma “cousin brother” dina, yana ciki yana asibiti shi ma, su kusan shida ne, suna Federal Medical center. Kuma duk mutananmu ne aka ji ma ciwo.

D .Murtala . ka ji abin da ya faru.

Katsina City News.: Police, ku a bangarenku sun fada maku akwai wanda aka kama?

D.Murtala :Ehh, bangarenmu akwai suna nan police headquarters, saboda abin da ya faru DPO na Musawa shi ya hada baki , da su Bala Abubakar, yan kudin ma da ake ba mutane daga cikin motarsa ake daukowa ana basu, sun hada baki da police ne, aka yi mana wannan wulakancin.

Katsina City News: Shi petitions da kuka rubuta, kun rubuta kun basu?

Hon. A’a mun ba Gwamna dai, yanzu muna saurare mu ji daga gare shi.

Katsina City News. Mun gode .

D. Murtala .Na gode, katsina city news.
Muazu hassan
Bashir Suleman
Suleiman Umar
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 081 37777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here