An bayyana Sanata Ibrahim Shekarau na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin dan takarar jam’iyyar a mazabar Kano ta tsakiya a zaben 2023.
A zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi a Gezawa hedikwatar karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano, ya fito takarar tikitin jam’iyyar ba tare da hamayya ba.
Shekarau wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne kuma sanata mai ci, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa NNPP bayan ya kasa samun tikitin takarar sanata na jam’iyyar na wani wa’adi na biyu.
Kawu Sumaila ya samu tikitin NNPP na Kano ta Kudu, yayin da Dr Abdullahi Baffa ya lashe tikitin NNPP na Kano ta Arewa.