Hukumar DSS ta kwato mahaifiyar dan takarar jam’iyyar APC a Kano ta tsakiya, sa’o’i 24 bayan an sace ta a wani yanki mai nisa na jihar Jigawa.
A safiyar ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Zaura da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano inda suka yi garkuwa da mahaifiyar AA Zaura a gidanta da ke kauyen Zaura.
Engr. Abdullahi Garba Ramat shugaban karamar hukumar Ungogo ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce jami’an tsaro ba su sanar da shi lamarin a hukumance ba.
Sai dai wani babban jami’in DSS da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa dakarunsa sun kubutar da Laure da wata tsohuwa da aka yi garkuwa da su kusan kwanaki goma.