Atiku Yana Wata Muhimmiyar Ganawa Da Gwamnonin PDP Akan Fitar Da Gurbin Mataimaki

0

Jaridar Leadership Ta Ruwaito Cewa Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, yanzu haka yana ganawar sirri da gwamnonin da aka zaba na jam’iyyar a Abuja.

An fara taron ne jim kadan bayan da tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023 mai zuwa.

Taskar Labarai ta gano cewa taron bai rasa nasaba da zaben wanda zai tsaya wa Atiku a zaben 2023.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da na Rivers, Nyesom Wike; Bayelsa, Douye Diri; Benue, Samuel Ortom; Sokoto, Aminu Tambuwal; Oyo, Seyi Makinde, da Bauchi, Bala Mohammed.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here