Kwankwaso Ne Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa 2023 – Shekarau

0

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2023, tsohon gwamnan jihar kuma jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Ibrahim Shekarau, ya Fadi Hakan a Abuja.

Da yake jawabi a wajen babban taron jam’iyyar NNPP da ke gudana a babban filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a yau Laraba, Shekarau ya ce ‘yan Najeriya na fatan samun shugabanci mai ma’ana don haka Kwankwanso ne zai lashe zaben shugaban kasa.

Shekarau wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ya ce “da yardar Allah Kwankwanso zai zama shugaban kasa a 2023”.

“Gaskiya shirinmu shine inganta rayuwar ‘yan Najeriya. ’Yan Najeriya sun dade suna jira, muna so mu canza ci gaba, mu canza gaskiyar ci gaba, mu canza rayuwar matasa zuwa ga mafi kyau.

See also  "Dr Mustapha Basirakka Ta Toshe, Saboda Zalincin Da kadinga Yiwa Mutane" - Bala Abu Musawa

“Muna so mu kawo shugabanci wanda zai anfani kowane dan kasa.

Babban taron jam’iyyar NNPP ya samu nasara saboda da yardar Allah Kwankwanso zai zama shugaban kasa a 2023,” inji Shekarau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here