‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 32, Sun Barnata Gidaje A Wani Sabon Hari a Kaduna.

0

Akalla mutane 32 ne rahotanni suka ce ‘yan bindiga sun kashe a wasu hare-hare da suka kai wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Ungwan Gamu, Dogon Noma, Ungwan Sarki da Maikori.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, amma Hakimin Kufena, Titus Dauda, ​​ya shaida wa Yan jarida cewa, an kai harin ne a ranar Lahadin da ta gabata, kuma mutane 32 ne suka rasa rayukansu yayin da wani coci da gidaje da dama suka ruguje.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar suna dayawa sun fara kai hari a Dogon Noma da sanyin safiyar Lahadi, inda suka kashe mutane da dama wadanda akasari maza ne, kafin su wuce kauyukan Ungwan Gamu da Maikori inda suka kuma kashe mutane tare da kona gidaje.

Hakimin gundumar ya kara da cewa an yi jana’izar wadanda abin ya shafa yayin da al’ummomin da abin ya shafa suka bar wajen saboda fargabar sake kai Wani hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here