Sarkin Kwatarkwashi da ke karamar hukumar Bungudu, Alhaji Ahmad Umar (mai-Kwatarkwashi), ya rasu a jihar Zamfara.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya ce basaraken ya rasu ne bayan doguwar jinya da yayi yana da shekaru 93 a duniya.
A cewar Balarabe, Sarkin ya rasu ne a jiya 9 ga watan Yuni, 2022, kuma an gudanar da sallar jana’izarsa a garin Kwatarkwashi mai tarihi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sarkin Musulmi Abubakar III ya nada Mai Kwatarkwashi a ranar 17 ga Maris, 1961. An fara nada shi hakimin kauye a garin Samawa da babban yayansa, wanda a lokacin ya kasance hakimi kafin ya hau karagar mulki a matsayin Mai Kwatarkwashi.
Shi ne sarki mafi girma kuma mafi dadewa a kan karagar mulki a jihar Zamfara yana da shekara 61 akan karagar mulki.