Wani Matashi Ɗan Damfara a yanar Gizo zai kwashe Shekara a gidan gyaran hali…
Wani Mai Zamba Ta Yanar Gizo Zai Yi Zaman Shekara Daya A Gidan Gyaran Hali A Port Harcourt
Mai sharia E. A. Obile na babbar kotun tarayya dake Port Harcourt, jihar River ya yanke wa Wani Mai suna Obu Gabriel Ebibo hukuncin shekara daya a gidan gyaran hali saboda laifin sojan gona daya kama shi dashi da zambar kudi.
Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin ne ranar Laraba 8 ga watan Yuni, 2022, bayan hukumar EFCC shiyyar Port Harcourt ta gurfanar da shia akan tuhuma biyu.
Wanda ake zargin dai Ya amsa laifin da aka tuhume shi da su bayan an karanto masa a gaban kotun.
Daganan sai Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin shekara daya ko ya biya tarar Naira dubu dari biyar