Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ki amincewa da kudi naira miliyan 50 da gidan rediyo na Ahmad Isah, wanda aka fi sani da “Ordinary President” ya bayar.
A wani shiri na rediyo da aka fi sani da Berekete family ya gayyaci shugaban kungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke da tawagarsa domin bayyana wa ‘yan Najeriya matsalolin da suka dade suna fuskanta tare da bayyana dalilin da yasa har yanzu kungiyar ke yajin aiki.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta ayyana yajin aikin gargadi na tsawon wata guda domin nuna adawa da rashin aiwatar da bukatun Kungiyar.
Amma a ranar 14 ga Maris, kungiyar ta tsawaita matakin da makwanni takwas, saboda gazawar gwamnati wajen magance bukatunta.
Mai masaukin baki ‘yan kungiyar na Berekete, Ahmad Isa a yayin tattaunawar da ya yi da shugaban ASUU ya ce ya kafa asusun ajiya na musamman a bankin TAJ domin tara kudade ga kungiyar, da nufin kawo karshen yajin aikin.