Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 37 A Wani Hari Da Suka Kai A Ƙauyukan jihar Benue.

0
55

Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a kauyen Igama a jihar Benue da safiyar wannan Lahadi, sun kashe mutane 37, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa jaridar PREMIUM TIMES.

Wani da ya tsira da ransa mai suna Ambrose Adah, ya ce maharan sun far wa al’ummar yankin ne a lokacin da shi da iyalansa ke shirin gudanar da taro.

Igama al’umma ce mai noma dake cikin karamar hukumar Okpokwu mai tazarar kilomita 160 daga Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Mr. Adah ya ce “A lokacin da muke shirin gudanar da Sallar Juma’a a safiyar Lahadi, makiyaya da yawa a kan babura suka mamaye mu.”

“An kashe ƴan unguwan mu galibi mata da matasa yayin harin.

“Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 37 kuma yanzu haka an ajiye su a babban asibitin St Mary’s Okpoga,” dake cikin karamar hukumar Okpokwu.

Mr. Adah ya bayyana wa jaridar PREMIUM TIMES ta wayar tarho a jiya Litinin cewa, “Makiyayan sun lalata min bungalow mai dakuna uku da wasu kayayyaki masu daraja”.

Ya kara da cewa: “an kone gidaje da dama kurmus,” yayin da sama da mutane 500 ne da harin ya rutsa da su ke neman mafaka a unguwar Ojigo, da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su.

Mr. Adah ya roki gwamnatin tarayya da ta kafa sansanin soji a yankin domin dakile ci gaba da kai hare-hare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here