AN KAI HARI CIKIN GARIN BATSARI TA JIHAR KATSINA

0

Misbahu Ahmad

@ katsina city news

A daren ranar litanin 13-06-2022 da misalin ƙarfe 08:30pm na dare ɓarayin daji masu satar shanu, garkuwa da mutane domin ƙarbar kuɗin fansa suka mamaye unguwar soli (unguwar kutare) dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Sun bi gidajen mutanen unguwar suna tambayar su wayar hannu da kuɗi, a haka ne suka sallama ma wani bawan Allah mai suna Hambali, inda sukayi ƙoƙarin tafiya da shi amma sai yayi ta maza ya samu wani icce ya buga ma ɗaya daga cikin su, dalili kenan da yasa suka yi harbi ta sharce shi ga kai.

Wasu daga cikin su kuma suna cikin unguwar suna aikin nasu, inda suka samu wani mai suna Mani Mada sukayi masu dukan kawo wuƙa da gindin bindiga, sannan suka kama mutum ɗaya Abdu mai doya, suka tafi da shi. Ganin biɗa ta ga rana yasa suka janye domin gudun martanin jam’an tsaro.

See also  Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar baiwa ɗalibai bashi a Nijeriya 

A wani labarin kuma da ya faru da rana tsaka a garin Kurmiyal ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi a bakin garin na Kurmiyal, matashin mai suna Salisu Lihidda ya shiga komar miyagun a gonar su dake gab da shiga garin su, inda suka yi garkuwa da shi, kuma har zuwa haɗa wannan rahoton ba’a ji ɗuriyar sa ba.

Mun kasa samun kakakin yan sanda na jahar katsina domin jin ta bakin shi.Amma ganau a batsari da kuma kurmiyal sun tabbatar mana da faruwar lamarin.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.taskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here