SANARWAR BAYAN TARO
A wani taron gaggawa da Mazauna Rukunin Gidajen Sardauna Estate dake cikin garin Katsina suka gudanar ranar Alhamis 02/10/1443 wanda yayi daidai da 02/06/2022, akan irin matsaloli da rohotanni marasa dadi da akeji ana gani dangane da ma’amalar Dalibai dake zaune acikin wannan Unguwa:
Jama’a sun tattauna sun cimma matsayar hana bada gidaje haya ga dalibai mata tare da kira ga wadanda suka gina Hostels a cikin wannan unguwar suka sanya yara mata dasu fitar dasu duk da cewar zasu iya maye gurbinsu da dalibai maza.
Wannan kuma ya faru ne ganin irin yadda
wadannan wuraren da mata suke zaune ke neman zama tamkar gidajen karuwai masu zaman kansu da hakan ka iya jawo tabarbarewar tarbiya da yaduwar alfasha da kuma bacin sunnan wannan unguwa.
Domin cimma wadannan qudurori, aka shirya daukar matakai kamar haka:
1. A rubuta, a nemi a zauna da hukumar Jami’ar Alqalam wadda galibin dalibannan anan suke karatu domin gano bakin zaren Don magance wadannan matsaloli.
2. A kai ziyara ga dau domin fadakar dasu abubuwan dake faruwa tare da neman goyon bayansu. acin masu gidajen haya cikin wannan unguwa
3. Estate manager zaya dauki alhakin zaqulo masu hostels a cikin wannan unguwar tareda gabatarda wadannan shawarwarin a garesu.
4. Mazauna wannan unguwa zasu yada wadannan matakai da suka dauka ta kafofin sadarwa domin sanar da alumma.
5. Za kuma a sanar da jami’an tsaro gameda wannan mataki da sauran masu ruwa da tsaki.
6. A karshe za’a fito da sabon tsari na yima hostels rejista acikin wannan Unguwa.
Wannan sanarwar ta fito daga bakin shugaban Special Taskforce Committee Dr. Dikko Bature Darma dauke dasa hannun shugaban mazauna wannan Unguwa Alh. Hamza Saleh Ketare da kuma Babban Magatakardan wannan Unguwa Arch. Yahaya Sufyanu Yar’adua.