Nasan tumasu karatu shine su ce wannan baiwar Allah tayi sa’ar sarauta ko? To da wannan din ma amma ba shi kadai ba ne dacenta a rayuwa ba akwai wasu kamar guda 12 ga su kamar haka:
1 Tana cikin tsaffi da suka ci duniya da tsinke cikin matsanancin koshin lafiya har shekaru 96 ba tare da ana jelan asibiti saboda cutar Cancer da sauran ciwuka ba
2 Ta girma da iyayenta ba tare da ta taba ganin wani abu mai suna rashi ko a nemi abu a ce maka babu ba
3 Shekarar ta 73 da igiyar aurenta har sai da tayi wa mijinta takaba, sabanin yadda auren manyan mutane ke saurin mutuwa a kasashen duniya
4 Bata taba binne ‘ya’yanta ba duka hudu sun girma a gabanta, Su ma sun ga ‘ya’yansu, ‘Ya’yansu ma sun ga Yayansu kuma duk tana raye wato dai ta ga tattaba kunne
5 Akwai Ikirarin ta fi kowane Sarki asali tunda ga asalin addinai har na sarauta inda a wata daawar ma har a Bangaren Musulunci ana danganta ta da jinin fiyayuen Halitta SALLALLAHU ALAIHI wasallam sannan a kiristanci Kakanninta ne suka kirkiri Darikar Anglican church
6 Hotonta ne a daya daga cikin kudade mafiya daraja a duniya wato (£) wanda kwaya daya yake daidai da Naira 757
7 Shekara 70 tana sarauta wanda ya bata daman zama Sarauniya mafi dadewa a tarihin Ingila da ma na duniyar Karni na 21, Ta ga bikin Silver, ta ga na Golden, ta ga na Diamond ta kuma sake ganin na Plantinium duka na sarautarta
8 Ta Mulki kasashe da dauloli 31 daya a zamanin da ake cewa rana bata taba faduwa a sarautar England ba, Kuma har yanzu cikin wadannan kasashen akwai 14 da ke karkashinta
9 Ita ce Wadda bata bukatar kowane irin ID card har Fasfo na tafiye tafiye kuma babu inda take bukatar Visa kafin ta shiga wata kasa
10 Bata taba amfani da sunan Mijinta a jerin sunayenta ba Sai dai shi ake alakantawa da Mijin Sarauniya
11 Tana jin sama da manyan yarukan duniya 7 ayayinda yaren kasarta ya fi kowane yare daukaka a duniya cikin karnin Bara da bana
12 Sau biyu ake Maulidinta a duk shekara, Wato ranar bikin haihuwarta na ainahi tayi bikinta da kanta sai kuma ranar bikin da an sabawa Duniya a tsakanin May da June
12 Ita ce Matar da ake sa ran idan ta Mutu har tattalin arzikin duniya sai ya girgiza, Domin za a sauke tuta sama da 14 a fadin duniya, Za a sauya hoton daya daga Kudaden duniya mafi daraja wato Fan, Sannan za a yi tururuwar zuwa zaman makoki da gaisuwar Mutuwa irin wanda ba a taba gani wannan karnin ba.
Sai dai kash!… Ta ki mutuwa