Allah Daya Gari Bamban: Kasar Thailand Ta Rabawa ‘Yan Kasarta Irin Tabar Wiwi Kyauta.

0

Kasar Thailand ta raba wa al’ummar kasarta irin tabar Wiwi kyauta da nufin kowa ya je ya shuka.

Ma’aikatar kula da harkokin lafiya ta kasar ce dai ta yi wannan aikin rabon irin tabar Wiwin, inda ake sa ran raba irin tabar wiwi guda miliyan daya kafin karshen wannan mako ga daukacin al’ummar kasar.

 

A cewar gwamnatin kasar, dasa tabar Wiwi zai taimaka gaya wajen bunkasa tattalin arzikin kasar musamman wajen samarwa kamfanonin har-hada magunguna na kasar da kayan aiki.

Kasar Thailand dai ita ce ya zuwa yanzu kasa ta farko a nahiyar Asiya da ta haramta zukar tabar Wiwi a fadin Kasar, amma kuma ta yi mi’ara koma baya wajen halastawa tare da rabawa jama’ar kasar irin tabar Wiwin da za su shuka.

See also  JAM'IYYAR APC TA FITAR DA RANAKUN FITAR DA YAN TAKARA

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, shin iya shukara tabar Wiwin ce kadai halasta ko kuwa hada zukar tabar Wiwin? Amsar da har yanzu ba mu samu amsar ta ba.

Hotuna daga: CGTN China

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here