SANARWA DAGA KUNGIYAR AFAN, RESHEN JIHAR KATSINA

0

Kungiyar manoma ta kasa, AFAN, reshen jihar Katsina ta samu labarin wasu dake ikirarin cewa sune shuwagabannin kungiyar.

Saboda haka ne kungiyar ke sanar da manoma da daukacin al’umar jihar cewa har yau kungiyar na karkashin shugabancin Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo wanda aka za6a a shekarar 2020, na wa’adin shekara biyar, har sai shekarar 2025 za a kara yin wani zaben.

Kungiyar tana gargadin masu ikirarin shugabancinta baa tare da shiga za6e ba, cewa zata dauki matakan shari’a a kansu.

Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, Shugaban kungiyar AFAN, reshen jihar Katsina, har ila yau shine kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here