WAKAR CIN ZARAFIN GWAMNA ….YAN SANDA NA BINCIKEN BADARU JIKAMSHI

0

Muazu hassan

@ katsina city news

Yan sanda na gudanar da bincike akan shugaban hukumar masaukin baki na katsina motal Alhaji Abubakar Badaru jikamshi akan wata waka da aka dauka gaban dakin taro na motel a wakar ana wasu kalamai na cin fuska da batanci ga gwamnan jahar katsina.Alhaji Aminu Bello masari.

Majiyarmu a rundunar yan sanda ta jahar katsina, ta gano,yan sanda sun fara gudanar da bincikensu bayan wani korafi da wani ya kai masu bisa zargin da akeyi ko yana da masaniya akan wakar.

Binciken na yan sanda ya kamo duk wadanda ake zargi da yada wakar.

Wanda daya daga cikin su ya tabbatar ma da yan sanda cewa.Abubakar Badaru jikamshi shugaban Motel shine ya tura masa wakar ya kuma ce masa ya yada ta.

Yan sanda sunyi nasara gayyatar jikamshi .Wanda ya rubuta jawabin yana da masaniya akan wakar .ya kuma ce sharrin shaidan ne.amsawar ya Sanya yan sanda sun tsare badaru jikamshi.wanda daga baya suka bayar dashi beli ga wani mutum mai mutunci a masarautar katsina.

See also 

Jikamshi ya sake rubuta wata takardar ta ban hakuri a wajen hukumar yan sanda.da neman a yafe masa.ya kuma Nemi gafara da yafiyar Wanda wakar ta shafa na zubar masa da mutunci.

Har zuwa rubuta rahoton nan, yan sanda basu iya kama Wanda yayi wakar ba,saboda ana zargin ya gudu zuwa kasar Nijar.

Kamar yadda wani musayar sakon waya da wani abokin shi ya tabbatar. Ya fada ma abokin cewa,zai bar katsina zuwa kasar Nijar don ya boye.

A iya binciken mu bamu iya samun wata alakar wakar da Alhaji Mustafa inuwa ba, ko kwamitin yakin neman zaben shi.a iya binciken mu basu da hannu a Sanya rera wakar.basu da hannu a yada ta.

Kwamitin yakin neman zaben Mustafa inuwa sun fitar da wata takarda inda suka nisanta kansu da wakar.

Masu bincike na hukumar yan sanda sun ce sun kammala aikin su .kuma suna jiran umurni na gaba.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.taskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here