NNPP A KANO TA KALUBALANCI GANDUJE akan bashin Naira bilya Goma

0

NNPP A KANO TA KALUBALANCI GANDUJE…akan bashin Naira bilya Goma..
Bashir Suleman
@ katsina city news
Jam’iyyar NNPP ta Kalubalanci Yunkurin Gwamnatin Ganduje, Kan Ciwo Bashin Biliyan Goma

A takardar da aka rabawa manema Labarai, wadda shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano Hon. Umar Haruna Doguwa ya sanya wa hannu.

Ya ta tambayi majalissar dokokin jihar Kano kan me yasa za ta amince da irin wannan bukata? Kasantuwar Gwamna Ganduje ya zama turun bashi.

Jam’iyyar ta kayan Marmari ta kalubalanci wannan bashi na Biliyan Goma da gwamnatin ke neman ciwo daga Bankin Access, domin sanar da kwamarorin tsaro na CCTV a jihar ta Kano.

Jam’iyyar ta Kara da cewa, idan aka lura da dumbin bashin da gwamnatin Ganduje ta ciyo wa jihar, ba tare da an gani a kasa ba, kawai dai yana amfani da karfin Iko wajen dorawa jihar dumbin bashin da zai durkusar da makomar yaran jihar.

Duba da yadda ta kasa biya daliban sakandire kudin kammala jarabawar fita, Wanda hakan ya haifar da tilasta barin makaranta ga daliban.

Ga kuma yadda ake ta fama da matsalar ruwa a jihar, amma a buge da ciwo bashin kafa kwamarorin tsaro na CCTV ba.

In ba za a manta ba, Dantakarar shugabancin kasa na Jam’iyyar NNPP Engr, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, ya taba sanya wadannan kwamarorin a jihar.

Amma sakaci na wannan gwamnatin ya Sanya sun lalace, shi ne yanzu take neman ciwo bashin zunzurutun kudi har Biliyan Goma domin kafa wasu sabbi, Wanda duk mai kishin Jihar Kano ba zai lamunci haka ba.

Don Muna kira ga majalissar dokoki ta jihar Kano da ta janye wannan lamuni, da ta Bai wa gwamnati.

Ya dace yanmalissar da su dubi bukatocin al’ummar ta hanyar aiwatar da abin da zai inganta rayuwar su, tun kafin a hambarar da gwamnatin a zabe mai zuwa na 2023

Sannan kuma Jam’iyyar ta Kira ga Bankina access da su jingina bayar da kowane irin bashi ga gwamnatin ta Ganduje.

Domin kuwa al’ummar jihar Kano shaida kan bashin Biliyan Hamsin da gwamnatin ta Ganduje ta ciwo domin bunkasa harkokin ilmi, amma sai ta karkatar da su wanda hakan haifar da jirangiyar daliba ba tare da sun iya kammala sakandire ba, domin rashin ko in kula ga fannin na ilmi.

Jam’iyyar ta Kara da cewa kawai da za a fake da guzuma ne a harbi karsana, a ciwo bashin Biliyan Goma, domin kuwa za a cike gibin makudan kudaden da gwamnatin ta salwantar a zabukan fitar da gwani na Jam’iyyar ta su ta APC ta gudanar.

Duba da haka, Muna kara Kira ga Bankunan kasuwanci da sauransu kungiyoyin bayar da lamuni na cike da wajen kasar nan, da su dakatar da baiwa gwamnati Ganduje bashi, domin gudun kassara sabuwar gwamnatin Mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here