Muazu Hassan
@ katsina city news
Gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello Masari CFR ya nada sabbin yan hukumar gudanarwar jami ar umaru Musa yar adua .kamar yadda wata sanarwa da Muhammad Yusufu Abubakar babban magatakardar jami ar ya Sanya ma hannu.
Sanarwar race an nada farfesa Mu’uta Ibrahim ya zama sabon shugaba.ya chanji Alhaji zakari Ibrahim Talban katsina.wanda lokacin sa ya kare.na shekaru biyar a wannan shekarar.
An Nada farfesa Usman Muhammad shu’aib da farfesa Junaidu Na aliya da Hajiya Talatu Nasir.a matsayin membobin sabuwar kumar gudanarwar jami ar.
Sauran membobin suna na da matsayin su .kamar su Dakta Bashir Abu sabe.wanda malaman jami a suka zaba ya wakilce su.
Sabbin yan kwamitin har sun fara aikin su inda sukayi zaman farko a farkon satin da ya kare.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
The links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779 081 37777245