Hotunan wani dan Najeriya da ya kammala karatu yana tura ruwa a jihar Taraba ya bazu a kafar sadarwa ta Twitter.
Mutumin mai suna Kawu Malami ya karanci engineering Agricultural and Environmental Resources a Jami’ar Maiduguri.
Daya daga cikin takardun shaidar kammala karatun digirin digirgir a fannin Injiniya a UNIMAID data bayar a ranar 15 ga watan Junairu 2015 kuma tana dauke da sunan Kawu.
Har ila yau, akwai takardar shedar malantaka masu zaman kansu da cibiyar malamai ta kasa wadda take a Kaduna, data bashi a shekarar 2001.
Kawu ya kuma mallaki satifiket a fannin fasahar Aided Design da Jami’ar Maiduguri ta bayar a shekarar 2009.
Wani da yai tsokaci akai ya ce mutumin mai dakinsa ne yayin da wani kuma ya ce mutumin ya bar aikinsa a Bauchi ya tafi Taraba.
Legit.ng ta tuntubi Sulayman Abubakar wanda ya yi ikirarin cewa Kawu abokin zamansa ne a UNIMAID. Ya tabbatar da gaskiyar labarin.