ANKAI HARI ƘAUYEN MAIƊORIYA TA BATSARI.
Misbahu Ahmad Batsari
@ katsina city news
A yau litanin 20-06-2022 da musalin 11:00am wasu mahara suka kai hari ƙauyen Maiɗoriya dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Inda suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Malam Hamza a gonar sa dake bakin garin, sannan sun yi yinƙurin sake cafke wani mutum amma Allah ya kuɓutar da shi. Da yake garin akwai makarantar sakandire mai suna G.S.S Ƴandaka-Ruma, wannan hari yasa ɗalibai da malamai shiga cikin tashin hankalin da baya misaltuwa, kowa na gudun ceton rai, daga bisani jami’an tsaro suka kawo ɗauki, amma dai basu iya ƙwato wanda ɓarayin suka ɗauka ba duk da ɓarin wutar da aka yi tsakanin su. Wani ganau ya bayyana mana cewa lokacin da yabi hanyar Ƴandaka yaga ɓarayin na fitowa daga wani tsauni suna gudu a ƙasa saboda ƙarar bindigogin jami’an tsaro da suke ji, saidai da yake su jami’an tsaron basu gan su ba, dalilin kenan da yasa ake zaton ɓarayin suna da yawa amma sai suka turo wasu kaɗan daga cikin su. Jama’a da yawa suna fatan gwamnati zata ɗauki mataki domin ceto yankin daga halin da suka shiga, domin ko a jiya lahadi saida ɓarayin suka tare hanyar shiga Ƴandaka daga Tashar Na-gulle sun tafi da wani Malamin makaranta malam Shamsu Garba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com