Hukumar NDLEA ta kama mutane 491 a Katsina

0

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce ta kai samame a gidajen sayar da miyagun kwayoyi tare da cafke mutane 491 da ake zargi a jihar katsina.

Mohammed Bashir Ibrahim, kwamandan hukumar na jihar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina a ranar Litinin a wani bangare na gudanar da bukukuwan ranar yaki da fataucin miyagun kwayoyi da Majalisar Dinkin Duniya (MDD). Ya ce, a tsawon lokacin da ake binciken, an kama mutane kusan 345, wadanda suka hada da maza 339 da mata.

Ya sake nanata cewa rundunar ‘yan sanda ta musamman da aka tura jihar daga hedikwatarta ta kasa ta kama mutane 146 a watan Yuni.

Sai dai shugaban hukumar ta NDLEA na jihar ya koka da cewa, “Abin bakin ciki da sama da kashi casa’in na wadanda ake tuhuma aka kama, suna tsakanin shekarun 15-40 ne.

Da yake yabawa Gwamna Aminu Bello Masari bisa dimbin taimakon da yake baiwa rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here