AN GAYYACE NI NAKI ZUWA NE……. Inji Umar Tata 

0

@ katsina city news

Alhaji Umar Tata Daya daga cikin wadanda suka Nemi Jam iyyar APC ta tsayar dasu takarar gwamnan jahar katsina. Ya bayyana ma jaridun katsina city news cewa taron da akayi na wadanda sukayi takara an gayyace shi amma yaki zuwa ne.

Umar Tata na bada amsa ne akan labarin da jaridar katsina city news suka buga akan zaman da akayi da wadanda sukayi takara don dinke barakar APC bayan zaben fitar da gwani.

Umar Tata yace shugaban jam iyyar APC ya turo masa da sakon ana gayyatar sa taro a gidan gwamnatin katsina da karfe sha biyu na Rana.

Yace na gani amma naki zuwa .ya bayyana cewa koda bai Bar APC ba.ba zai halarci taron ba.don bai aminta da wadanda suka Kira taron ba.

yace in lokacin Magana yayi zai fede biri har wutsiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here