Wani dattijo mai shekaru 51, Alhaji Usman Madaki, ya fara tattaki daga Bauchi zuwa Legas domin murnar nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki.
Madaki, wanda kuma dan asalin Bauchi ne, an ce ya fara tattakin ne a ranar 10 ga watan Yuni, 2022, kuma ana sa ran isowarsa Legas a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni, 2022.
Rahotanni sun ce ya isa Ilorin, babban birnin jihar Kwara kuma ana sa ran zai isa Ibadan a ranar Alhamis 23 ga watan Yuni, 2022.
Madaki, Yayi magana a Ilorin a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni, 2022, ya ce ya fuskanci kalubale da dama a tsawon tafiyar, da suka hada da zargin yunkurin yin garkuwa da mutane ne tsakanin Kafanchan da Zangon Kataf.
“Ina so in gana da Tinubu a Legas domin nayi masa murna kan nasarar da ya samu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC,” in ji shi.