WASAN KWAIKWAYO: Wani Lauya dake kare haƙƙin Ɗan’adam ya shiga Kotu da kayan Masu bautar gargajiya a Abuja

0

Fassara Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Majiyar Daily News Nigeria

A ranar Alhamis ne wani lauya mai kare hakkin dan Adam da ke Legas, Malcom Omoirhobo ya tayar da Ƙura a kotun koli da ke Abuja, yayin da ya fito cikin rigar gargajiya ta wani “limamin Olokun” domin halartar zaman kotu.

Lauyan ya ce ya shigo kotu ne da kayan Bautar a irin wannan yanayi domin yin amfani da muhimman hakkokinsa na dan Adam biyo bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na bai wa ‘yan Najeriya damar bayyana yadda suke Ibada da kuma amfani da hijabi a makarantu da wuraren taruwar Jama’a.

Idan dai ba a manta ba a ranar Juma’a ne kotun koli ta amince wa dalibai mata musulmi sanya Hijabi zuwa makaranta a jihar Legas.

Biyar daga cikin bakwai na kwamitin da kotun ta zauna kan shari’ar ta yanke hukuncin sanya hijabi yayin da sauran mambobin biyu suka nuna rashin amincewarsu.

Lauyan wanda ya isa kotun da misalin karfe 9:05 na safe, ya haifar da wani yanayi a harabar kotun inda wasu lauyoyin da ke zaune suka yi mamakin ganin sa sanye da kayan gargajiyar kamar mai sana’ar tsire.

Lauyan da ya samu shiga kotun ba takalmi  da fuka-fukan da ke makale wuyan rigar sa.

Sanye yake da gora a wuyansa da garwashi da jajayen lulluɓe a kugunsa.

Ya ja kunnen jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaron da suka tunkare shi da nufin su fitar da shi, ya ce yana da hakkin ya zo kotu da kayan sa na gargajiya ba tare da tsangwama ba kamar yadda aka yanke hukunci.

Ba zato ba tsammani dai an dakatar da shari’ar kotun, kwatsam sai da alkalin kotun ya sanar da cewa za su dan yi hutu.

Ko da yake ba a iya gano ainihin abin da ya janyo dalilin shiga gajeren hutun ba.

Lamarin dai ya jawo dimbin jama’a da suka yi dafifi a harabar Kotun domin ɗaukarsa Hoto da wayoyinsu

Malcom wanda ya yi jawabi ga manema labarai ya ce, “Ina matukar godiya ga Kotun Koli a makon da ya gabata a ranar Juma’ar da ta gabata ta yanke wani hukunci mai ma’ana wanda ya inganta sashe na 38 na kundin tsarin mulkin kasar. Haƙƙinmu ne na ’yancin tunani, lamiri, da addini. Cewa za mu sami yancin fadin albarkacin bakinmu a makarantunmu da kotuna. An cimma wannan shawarar a ranar Juma’a kuma hakan ya ƙarfafa ni.” Lauyan ya ƙara da cewa

“Saboda ni ’ Ɗan gargajiya ne kuma haka nake bauta. A bisa hukuncin da kotun koli ta yanke, haka zan ci gaba da yin sutura a kotu domin ni mai bin “Olokun” Ubangijin Kogo ne.

Malcom ya ce ma’anar hukuncin shi ne, kowane dan Najeriya da ya hada da Likitoci, ‘Yan sanda, Ɗalibai Soja, da ‘yan Jarida, yanzu za su iya sanya salon Ibadarsu a wuraren taruwar jama’a.

Ya kara da cewa bai ki amincewa da hukuncin ba sai dai ya yi farin ciki da hukuncin domin ya karfafa da kuma wadatar da ‘yancin ‘yan Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya tanadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here