Kurtun Dansanda ya maida Dalolin Maniyyata Aikin Hajji da ya tsinta a katsina

0

Wani kurtun Dansanda mai suna Nura Mande, na sashen sufuri na rundunar Yansandan Nigeria reshen jihar katsina, ya Burge Hukumar Alhazai da Alhazan bana a daren Jiya, lokacin tantance Alhazan 2022, a hukumar Alhazan jihar katsina, a Sansanin Hukumar Alhazai da ke titin sarki Abdurrahman da ke katsina.

PC Nura Mande ya tsinci Dala 800, guzurin wata maniyyaciya daga Ƙaramar hukumar Kusada mai suna Hadiza Usman Chamiya, sanar da hukuma.

PC Nura ya damka Wannan kudi ga hukumar Alhazai ta hannun Daraktan sashen mulki na hukumar, Alh Sada Salisu Rumah, inda aka damka wa maniyyaciyar kudinta.

Dansanda Nura ya ce tsoron Allah ya sa a zuci sama da bukatar kudin.

Da ya ke amsar kudin da damka wa mai su, Alh Sada Rumah ya yaba da kyawon hali da nuna gaskiya.

Ya ce shugaban hukumar Alhaji Suleiman kuki zai sanar da rundunar yansandan jihar katsina kan Wannan hali na kwarai da ya nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here