NEMAN MATAIMAKIN GWAMNA A JAM IYYAR PDP
……An tantance mutane uku
Muazu hassan
Wani kwamiti da Dan takarar gwamna a jam iyyar PDP Alhaji Yakubu Lado Dan Marke ya kafa don fitar masa da Wanda zai mara masa baya a matsayin mataimaki, ya fitar da mutane uku.
Kwamitin Wanda yake karkashin Alhaji Umar tsauri,ya bada shawarar mutane uku.mutanen sune. Alhaji Ahmad Aminu yar adua.Alhaji Sanusi abdu fari da kuma Alhaji Mustafa Musa yar adua.
Wadannan sunaye sune aka ba kwamitin uwar jam iyya ta kasa don ta tace ta fitar da mutum.
A jiya laraba uwar jam iyya ta gama ganawa da duk wadanda aka bayar da sunayen nasu.
Majiyarmu tace kwamitin yana bada shawarar a dau Ahmad Aminu yar adua.amma shi Dan takarar Alhaji Yakubu lado ya fi Natsuwa da Alhaji Sanusi Abdu fari.
Duk shawarar da kwamitin uwar jam iyya ta kasa ta tsayar da Amincewar dan takara za a sani zuwa gobe jumma a .24/6/2022.
Wata kila daga nan zuwa asabar za a iya sanin wa zai marawa Yakubu lado baya a takarar shi ta neman gwamnan katsina
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com