KANNYWOOD: Bikin Lilin Baba Da Ummi Rahab Ya Haifar Da Cece Kuce.

0

A ranar Asabar da ta gabata 18 da ga Yuni ce aka yi bikin auren mawaki Shu’aibu Ahmed Abbas wanda aka fi sani da Lilin Baba da amaryarsa Ummi Rahab.

An daura auren ne a Tudun Murtala, ofishin NEPA hannun riga da Bala Kasa, Tudun Murtala, Kano

Adam a Zango bai je bikin ba, kuma bai yi aike ba Sai dai duk da cewa an yi biki iya baki, yan Kannywood da dama sun nuna kauna a wajen bikin da kwallon kafa da aka buga da casun da aka yi, amma baa ga jarumi Adam A. Zango ba, wanda shi ne asalin ubangidan jarumar a masanaantar.

Idan ba a manta ba, Ummi ta fara fitowa a fim ne a fim din Ummi na Abdul Amart Maikwashewa tare da jarumi Adam A. Zango. Bayan dogon lokaci ba a ganta ba, sai ta sake dawowa masana’antar tare da ubangidanta Adam A. Zango, kamar yadda Jaridar Aminiya ta Ruwaito.

See also  Hotunan rahama sadau na cika Shekara 29 ya janyo ce-ce kuce a yanar gizo

Sai dai ba su dade ba, sai rigima ta barke a tsakaninsu, inda jarumin ya cire ta a cikin fim dinsa mai dogon zango na Farin Wata.

An yi ta tsammanin Adamu aa wajen bikin, amma ba a gan shi ba. Sannan Majiyar ta leka shafinsa na Instagram, inda ta lura jarumin
bai ce komai ba game da bikin, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce.

Rashin zuwan jarumin bai rasa nasaba da rashim fahimtar da suka samu a baya, inda wasu suke ganin ya kamata a ce ya huce.

Ummi ce matar Lilin Baba ta biyu

wani bincike ya gano cewa Ummi Rahab ce matar mawaki Lilin Baba ta biyu.

Wannan ya kore muhawarar da aka rika tafkawa a kafofin sadarwa cewa ita ce kadai matarsa. Kuma tuni aka kai amarya dakinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here