DSS SUN KAMA MAWAKIN DA YA YI MA MATAN KANNYWOOD WAKA

0

Biyo bayan wani korafi da wasu matan Kannywood suka aikewa Shugaban MOPPAN na Kasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, mai taken: “KORAFIN CIN ZARAFI DA WANI MAWAKI MAI SUNA ‘SUFIN ZAMANI,” a cikin takarda, wadda tsohuwar jarumar fim Wasila Isma’il ta sanya wa hannu, a madadin Matan Kannywood, MOPPAN, a cikin gaggawa ta tsunduma cikin binciken korafin, daga bisani, ta rubutawa Hukumar DSS, domin ta yi abin da ya dace.

Bayan da MOPPAN ta aikewa hukumar ta DSS ne, hukumar ta yi nata ayyuka din, kana ta nemo gami da cafke mawakin.

A ranar Larabar nan 22 Yuni ne, hukumar ta kamo Sufin Zamani, kana kuma ta bayar da belinsa a ranar Alhamis (23 ga Yuni), bisa wadannan sharudda:

1. Zai yi bidiyo da Audio na ban hakuri da kuma karyata kansa game da wakar batancin da ya yi.

See also  "Idan na zama 'yar Majalisa Duk Namijin da aka kama yayi Fyaɗe sai an Dandaƙe shi." ---Aisha Balarabe Alaja Katsina ta tsakiya--

2. Zai yi waka kishiyar wacce ya yi, wato ya bi matan kannywood, ya fadi alherinsu kuma ya nuna masu zaman aure ne.

3. Zai rubutawa MOPPAN takardar ban hakuri

4. Zai rubutawa hukuma undertaking cewar ba zai kuma yin batanci ga duk wani dan fim ba.

5. Bayan yayi wannan kuma hukumar DSS za ta yi masa hukunci da ya dace, domin yayi musu karya a farkon kamun da aka yi masa.

Duk wannan ya biyo bayan amincewa da ya yi cewa ya aikata laifin.

Sa hannun
*Al-Amin Ciroma*
*Kakakin MOPPAN na Kasa*

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here