MAJIGIRI ZAI TSAYA TAKARAR DAN MAJALISAR TARAYYA A MASHI DA DUTSI.

0

muazu hassan

@ katsina city news

Akwai yiyuwar Alhaji Salisu Yusufu Majigiri shugaban jam iyyar PDP a yanzu kuma Wanda ya sha kaye a zaben fitar da Dan takarar gwamna a PDP, ya koma yayi takarar Dan majalisar tarayya a kananan hukumomin Mashi da Dutsi.

Majiyarmu a cikin jam iyyar PDP ta tabbatar mana yanzu haka tattaunawa tayi nisa akan hakan.

A tsarin Wanda yaci zaben takarar a PDP Alhaji sule Yusuf shabeji daga karamar hukumar Dutsi zai janye ya rubuta ma hukumar jam iyyar sa da hukumar zabe.su kuma jam iyyar zasu maye sunan sa da majigiri.

Wata majiya ta tabbatar mana har anyi hakan a satin da muke ciki.majiyarmu tace tsakanin talata zuwa Alhamis hedkwatar jam iyyar PDP ta kasa ta aika ma suna INEC da sunan Majigiri a matsayin chajin sule Yusufu. Bisa kaidar da dokar zabe ta tanada.

Wani na kusa da Majigiri ya tabbatar mana da labarin, cewa ana wannan maganar amma ba a kammala ta ba.

Yace Majigiri Dan siyasa ne, mai son jama arsa da cigaban su amma ba girman Mukami ba.

Yace majigiri yana neman ya zai kawo cigaba ne ga al umma ba wai wane girman mukami ba,shi ya sa muka Sanya ya amince da wannan tsarin.

Ya kara da cewa shima Wanda yaci zaben takarar Alhaji sule Yusufu ba ya shigo siyasa bane don mukami ya shiga ne don taimakon al umma .

Idan wannan takarar ta tabbata, majigiri zai shiga kundin tarihi.na yayi rike shugaban jam iyya,yayi takarar mataimakin gwamna.yayi ta gwamna.yanzu zai yi ta Dan majalisar tarayya.

Majigiri zai kara da Babban yaron shi a siyasa,Alhaji Mansur Ali mashi a jam iyyar APC. Mansur Ali mashi ya koyi horon siyasa ne a wajen Majigiri.

Don haka akwai yiyuwar a zaben 2023 a yi karon battar karfe tsakanin yaro da ubangidansa a zaben Dan majalisar tarayya na mashi da Dutsi.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here