Kimanin maniyyata 545 Yan jihar katsina suka Isa kasa maitsarki

0

Kimanin maniyyata 545 Yan jihar katsina Jirgi na biyu ayau suka tashi daga filin sauka da tashi na Umaru Musa Yar’adua International airport zuwa kasa maitsarki.

 

Jirgin Wanda ya tashi da misalin karfe 3.51am yanzun haka sun sauka filin sauka da tashi na King Abdulazeez International airport Jeddah lafiya kalau.

 

Amirul Hajj justice Musa Danladi Abubakar tare da Babban Daraktan Hukumar Alhaji Suleiman Nuhu Kuki sun Yaba da kwazo ga jami,’an dake gudanar da tantance maniyyatan cikin lokacin batare da samun wata matsalaba.

 

Wannan shine karo na biyu da Ake samun Nasarar ta-da jirgin Alhazai cikin lokacin ba Kuma tare da samun wani tsaiki ba Wanda zaya Sanya jinkiri ga masu jiragen.

See also  37 NEW FIGHTER JETS AND ATTACK HELICOPTERS HAVE BEEN PROCURED AGAIN BY THE BUHARI ADMINISTRATION!

 

Yanzun kimanin maniyyata 1,099 daga jihar katsina su ke a kasa maitsarki.

 

A Wani labarin Kuma Alhazan jirgi na farko na Jihar katsina dake birnin Madina na cigaba da gudanar da ibadun su lami lafiya.

 

Yanzun haka yawancin Alhazan guda 554 duk sun kammala ziyarar su kamar yanda Addinin musulunchi ya tanada.

 

A Wani bangaren Kuma mallam da gwamnatin jihar katsina a karkashin Jagoranchin Rt.Hon Aminu Bello Masari ta dauki nauyin tura was Domin Alhazan jahar na cigaba da dada kar da maniyyatan yanda zasu guda nar da aikin Hajjin su Domin su Sami Hajj Mabrur.

 

PRO PWBKT BADARU BELLO KAROFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here