Muazu hassan
@ katsina city news
Tsohon Dan Majalisar tarayya a kananan hukumomin kurfi da Dutsinma Alhaji Danlami Kurfi ya bayyana cewa nan da watanni kadan zasuyi ma jam iyyar APC zigidir.suyi mata korar kare.
Ya bayyana haka ne, a wata tattaunawar da jaridun katsina city news suka yi dashi a ofis sa dake katsina.
Dan kasuwa kuma Dan siyasa ya bayyana cewa, PDP a matakin jaha da kuma kasa suna ta tattaunawa da jiga jigan APC da aka ci Amanarsu da wadanda aka bata ma Rai.
Danlami yace, Da yawan su.sun ayyana lokacin da zasu shelanta ficewarsu.don haka fitar zata rika kamawa lokaci, lokaci ne.wasu ma sai a daren zabe.
Danlami,ya kara da cewa daga cikin yan APC wasu, za suyi zaman su a cikin ta suyi ma PDP aiki lokacin zabe.
Danlami yayi misalta jam iyyar APC da jirgin da ya fashe a tsakiyar teku kuma ya fara Nutsewa.yace abin da ya rage wajen tsira,tsirar itace jam iyyar PDP.
Danlami yayi Kira ga Al ummar katsina, su san azabar da suke sha na rashin Tsaro.su kori jam iyyar APC .su kuma zabi PDP
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 0813777779