Kamfanin MTN zai biya mawakin Najeriya N20m saboda amfani da wakarsa a matsayin kiran waya (Caller Tone) ba tare da izini ba.

0

Kamfanin MTN zai biya mawakin Najeriya N20m saboda amfani da wakarsa a matsayin kiran waya (Caller Tone) ba tare da izini ba.

Wata babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta umurci katafaren kamfanin sadarwa na MTN Nigeria da ya biya wani mawakin nan na Abuja, Liberty Williams  naira miliyan ashirin bisa laifin keta haƙƙin mallaka Wato (copyright).

Rahotanni sun bayyana cewa, Mai shari’a Mary Ojukwu a lokacin da take yanke hukuncin a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, 2022 ta bukaci kamfanin sadarwa na MTN da su kuma bayar da ribar da suka samu na tsawon shekaru uku akan Wakar.

Mai shigar da karar ya zargi MTN da sayar da wata waka da ya yi a watan Yulin 2013 a matsayin sautin ringi.

See also  APC Ta Cire Mutun 10 Dake Neman Takarar Shugabancin Ƙasa

Ya roki kotu da ta bayyana cewa sayar da wakar da MTN ya yi ba tare da amincewarsa ba ya zama cin zarafi a kan hakkin mallaka Wato (copyright).

Mai shigar da karar ya yi zargin cewa kamfanin na MTN tare da hadin gwiwar kamfanin No Where to Run Entertainment Company, ya bayar da wakarsa mai suna “Love is everything” ga miliyoyin masu amfani da shi a matsayin sautin ringi da kuma kiran waya ba tare da izininsa ba.

Mai shigar da karar ya roki kotu da ta biya shi Naira miliyan 200 a matsayin diyya na gaba daya da kuma Naira miliyan 100 a matsayin diyya mai tsanani da kuma hukunci a kan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here