Muazu hassan
A ranar 5 ga watan yuni ne lauyoyin Alhaji Bala Abubakar musawa .Mataimakin shugaban jam iyyar APC ta jahar katsina suka shigar da karar Alhaji Mamuda lawal Musawa Wanda ake Kira da Mai zamani a kotun majistire ta uku dake kan titin Hassan Usman katsina.
Lauyoyin Bala abu musawa na neman kotun da ta bi masa hakkin sa na na bata masa suna da yi masa karya Wanda ya zubar masa da mutunci.wanda suke zargin Alhaji Mamuda ya aikata a wani rubutun da yayi ya kuma kama suna bala abu musawa, Baro Baro.
A ranar 9 ga watan yuni akayi zaman farko.wanda lauyan Wanda ke kara ya halarta amma Wanda ake tuhuma bai zo ba, kuma bai turo wakilin lauyansa ba.
Alkalin ya daga Shari ar zuwa Alhamis 30 ga Watan yuni,Wanda ya bada umurnin a tabbatar an kai ma Wanda ake karar takardar sammacin.ma aikacin kotu ya tabbatar da kai sammacin.
A zaman ranar Alhamis 30 ga watan yuni.bayan zaman kotun koda aka Kira shari ar, sai alkalin ya bayyana yana da bayani da zaiyi akan Shari ar.
Alkalin yayi jawabin cewa bisa wasu dalilai na kashin kansa.wanda ba dole bane sai ya bayyana su gaban kotun.ya tsame kansa daga wannan Shari ar .
Alkalin ya bayyana cewa, ba zai iya wannan Shari ar ba.don haka kotun sa ta tsame kanta daga sauraren karar da zaman Shari ar.
Alkalin ya Nemi wadanda ke karar su Nemi wata kotun da zata iya sauraren karar, su shigar da sabuwar kara a waccar kotun.
Daga nan Alkalin yace ya rufe wannan Shari ar a kotun sa .yayi masu fatan Alheri, ya cigaba da sauran Shari un dake gabansa.
Asalin matsalar ta faro ne,daga zaben fitar da Dan takara da akayi, na Wanda zai tsaya ma jam iyyar APC takarar Dan majalisar tarayya a mazabun Musawa da Matazu.
Anyi rikici kafin fara zaben, har aka kashe wani matashi Dan matazu mazaunin jahar Kano.
Bayan rikicin Alhaji Mamadu lawal ya rubuta wata takardar korafi ga gwamnan katsina,jami an tsaro, Hukumar zabe da kuma uwar jam iyyar APC.
A rubutun yayi wasu kalamai,wadanda lauyoyin bala abu suka ce, sun bata sunan Bala abu musawa. Daga ciki har da zargin Bala abu ne ya kawo yan dabar da suka kawo hargitsin gabanin zaben .
Akan wannan takarda ne, Alhaji Bala abu musawa ya umurci lauyoyin shi su bi masa hakkin shi.su kuma suka shigar da karar an bata ma Bala Abu suna .Shari ar ko zamanta ba a fara ba, Alkalin yace ba zai yi Shari ar ba,akai ta wata kotun.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08134777245