“Rashin Adalcin Jam’iyyar APC yasa na fita daga cikinta…….Musa Gafai

0

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 🗞️

 

Tsohon Ɗan takarar Kujerar Majalisar wakilai ta tarayya daga mazaɓar ƙaramar Hukumar Katsina, Honarabul Musa Gafai, ya bayyana wa Jaridun Katsina City News Dalilin sa na ficewa daga jam’iyyar APC mai Mulki, zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

 

Gafai ya zargi wani abokin takarar sa da suka fito neman kujera ɗaya da ita kanta jam’iyyar da tafka rashin Adalci. Inda yace dalilin ficewarsa kenan. Da yake zantawa da Katsina City News a ranar Asabar 2 ga watan yau 2022. Hon. Gafai yace “Da farko du wata Doka da ƙa’ida da jam’iyya ta shimfita tun daga mataki na mazaɓa (Ward) zuwa ƙaramar Hukuma, (Local Government), State zuwa na ƙasa (National) na bisu. Inda na sayi Form na ciki kuma na maida kamar yanda Doka ta tanada. A yanda Doka ta tabbatar cewa Ɗan takara ko wani mai ruwa da tsaki, ko wani mai ganin yanada Al’umma, Doka ta hana, ya ɓoye masu yin Zaɓe, wato (Delegates), Amma sai muka samu labarin cewa wani daga cikin wanda muke zargi ya ɓoye Delegates, wannan na ɗaya daga cikin ni abinda nake gani ba’ai mun Adalci ba.” Inji Gafai.

 

Honarabul Gafai ya kara da cewa ” Sannan abu na biyu kuma, Ciyaman na jam’iyya da kansa ya turo mun cewa za’ayi zabe a Katsina Local Government Secratariat, daga bisani kuma sai aka canza aka ce za’ayi a Local Government Service Commission. Ni a matsayi na na ɗan takara ya kamata ace ma ni ga dalilin samun wannan canji da akayi. Muna nan Local Government Service Commission da karfe goma na safe kuma sai aka ce ma na, an maida shi a Filin wasa na Karkanda, wato (Karkanda Stadium) da karfe goma zuwa sha biyu, a nan ma ba’a sanar damu dalilin yin haka ba, muna nan dai muna ta jira, karfe sha biyu sai aka ce mana ai am maida zaɓen kafin a taso daga Masallaci, muna nan muna ta faman jira, amma ba malaman zaɓe babu masu zaɓe da ni da Ɗan Majalisa mai ci, Hon Salisu Iro, da Abdulrashid Abba Ali, karshe ma sai da muka rasa sallar juma’a. Saidai muka je can Ɓatagarawa, inda ake sallah biyu da rabi, bayan mun dawo muka iske babu alamun zaɓe babu Dalilin shi, har karfe hudu zuwa biyar. Can daga bisani sai muka ga an fara kawo Delegates a cikin motoci ciki harda motar wanda muke zargi, kafin nan kuma sai aka kawo ƙauraye da Adduna suna ta busa ƙaho suna buga makamai, wanda kuma haka ba daidai bane.” Inji Gafai.

 

A karshe yace suna wajen sai suka ji ance angama zaɓe kuma koya ya yarda da zaɓen, yace “wannan ni yana cikin abinda naga cewa ba’ai mani Adalci ba, kuma shine Dalilin da yasa na bar jam’iyyar APC.” Inji Gafai.

 

Kafin nan Honarabul Musa Gafai ya Shaidawa Katsina City News yanda ya rubuta takarda ƙorafi har ga Kwamishinan’yansanda amma ya kawo haɗa wannan rahoto babu wani mataki da aka iya ɗauka. Yace “wannan shine Dalili na, ba wai don na faɗi zaɓe ba”

 

A ƙarshe Musa Yusuf Gafai ya yi kira ga Al’ummar Jihar Katsina da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata su su marawa Senata Yaqubu Lado Danmarke baya a matsayin Gwamnan jihar Katsina da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa, yace Dukkanin waɗannan ‘yan takarar namu suna da Cancanta da zasu iya jagoranci, na kowane fanni, Inji Alhaji Musa Gafai.

 

Akwai Cikakkiyar Firar ta Bidiyo zamu kawo maku ita a shafukan mu, na sada zumunta, ku kasance da mu a Katsina City News 🗞️

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here