Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City New
Wata Cibiyar horo da bada kayan sana’a ga Matasa Maza da mata a katsina Mai suna El’ladan Foundation tayi bikin yaye ɗalibai da ta koyawa sana’o,i don dogaro da kai a ranar Lahadi 3 ga watan yau na 2022 da muke ciki. Taron da ya gudana a harabar Makarantar Firamare ta Garama, da misalin karfe 11 na ranar ta Lahadi ya samu Bakuncin Injiniya Muttaqa Rabe Darma, da ya gabatar da ƙasida mai taken Muhimmancin koyon sana’o’i ga rayuwar Al’umma. Sai Matashi Comrade Ahamed Suleman, tsokaci akan gudummawar Matasa akan cigaba ta hanyar kwarewa. Shehun Malami, Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) Ƙasida akan Muhimmancin taimakon Maraya.

Shugaban ƙaramar Hukumar Katsina, da ya samu halartar taron Alhaji Aminu Ashiru kofar sauri yayi tsokaci akan irin gudummawar da Ofishin sa na ƙaramar Hukumar Katsina yake badawa akan Matasa da sana’o’i, inda yace sun zauna da ƙungiyoyin Matasa domin ƙara basu shawara akan abinda ya dace a yiwa matasa don samar masu da cigaba, sannan kuma sun zauna da hukumar Ilimi ta Katsina akan samar da wani Kwas, na karatu da zai koyar da sana’a kamar Entrepreneur da zai koyar da ɗaliban Firamari sana’a a ajin su na ƙarshe.

Akwai wakilin Hakimin Kusada Alhaji Nuhu Yashe, Shugaban Ƙungiyar KDF da sauran Kansilolin da suka rufawa Shugaban ƙaramar hukumar baya. An koyar da Matasan nau’in sana,o’i daban daban kamar irin su Ɗinki, Saƙa, haɗa Takalma, na Maza da na Mata, Jikkuna, na Mata, Zannuwan gado, Abincin Zamani da Cake ? na Bukukuwa, Ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa, haɗa Kayan kamshi, Iri-Iri da Turaren wuta. Da sauransu


Mutane da dama sun bada gudunmawa a wajen domin wannan makaranta taci gaba, ta hanyar kaddamar da kayayyakin na sana’a don karfafa gwiwa ga ɗaliban, inda Wakilin Hakimin Kusada kuma sarkin Fulanin Kusada ya sayi Takalmin da daliban suka ƙera akan kuɗi naira dubu ɗari biyu da hamsin, Aminu Ashiru Ciyaman na ƙaramar Hukuma ya sayi Takalmi akan ƙud naira dubu hamsin, inda wasu sun aiko da gudumawa iri daban daban ga ita wannan cibiya. A karshe shugaban cibiyar ta horas da sana’o,i Malam Buhari Ibrahim ya yi jawabin godiya gami da gabato da wasu sakwannin, aka sallami kowa.