Ansamu Bullar Cutar Kyandar Biri ta farko A Jahar Katsina.

0

Kwamishinan lafiya Yakubu Danja ya tabbatar da haka a lokacin kaddamar da rabon magunguna kyauta ga kananan hukumomi 34 na Jahar ga cibiyoyin lafiya.

 

Ya ce gwamnati ta himmatu wajen wayar da kan dukkan kungiyoyin bayar da agajin gaggawa, domin dakile ci gaba da yaduwa a jihar.

 

A cewar kwamishinan lafiya jihar yace akwai kimanin mutane 15 da ake zargin sun kamu da cutar, wadanda aka kai samfurin su Abuja, kuma suna jiran sakamakon.

 

Ya kara da cewa, domin tunkarar cutar da kuma kwalara da sauran cututtuka masu alaka da damina, gwamnatin jihar ta yanke shawarar raba magunguna ga kananan hukumomi 34.

See also  Hukumar shige da fice ta Najeriya ta kori ma’aikata 8

 

Kwamishinan ya kuma duba kayan aikin agajin gaggawa da ake kira ‘Call Centre’, da na’urorin sanyaya masu dauke da na’urorin hasken rana 140, wanda hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa ta bayar, domin tabbatar da karfin alluran rigakafin, da kuma rage kudin da ake kashewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here