Haɗuwar Makarantun Firamare 10 don gasar Kacici-kacici a Safana, Gumi da Annatija sunyi Zarra…

0

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News ?️

A ranar Litanin 4 ga watan bakwai ne, ɗan siyasa kuma tsohon Ɗantakarar Kansila a mazaɓar Safana “A” a ƙaramar hukumar Safana, ta jihar Katsina, Hon. Zilkifilu Nura, shine wanda ya shirya gasar ta Kacici-kacici wadda aka fara gudanarwa tun daga ranar Ashirin da biyar ga watan shida 2022 aka ƙarƙareta a ranar 4 ga watan 7 (Ranar Litanin) a ranar ta ƙarshe an gudanar da gasar a tsakanin Makarantu biyu da sukayi Zarra a cikin goma da suka shiga gasar a baya. Makarantun da sukayi Zarra a cikin goma kuma suka fafata tsakaninsu, sune: Gumi Primary School, da Annatijah Primary School, inda a karshe Annatijah Primary School tazo ta ɗaya da Maki ɗari da biyu 102 inda Gumi Primary School tazo ta biyu da maki ɗari da ɗaya da rabi, 101/2.

An gudanar da gasar ne gaban manyan baƙi kuma Iyayen ƙasar ta Safana, da Suka haɗa da Yariman Katsina, da ya samu wakilcin Alhaji Yahaya Barau, Sakataren Ilimi na ƙaramar Hukumar Safana (E.S.), Shugaban tsaro na Jami’ar Gwamnatin tarayya dake Dutsin-ma, Ciyaman na ƙaramar Hukumar Safana da ya samu wakilcin Shugaban Kansilolin yankin, Sai Farfesa Bashir Aliyu Sallau daga jami’ar Gwamnatin tarayya ta garin Dutsin-ma. Da sauran baƙi iyayen yara da ɗalibai.

See also  Filin Kwallon Da Jirgin Kasa Ke Bi Ana Tsaka Da Wasa

Da yake jawabi a wajen taron bayan tabbatar da waɗanda sukayi Nasara, Farfesa Bashir Sallau ya nuna farincikinsa gami da yaba namijin kokarin Hon. Zulkifilu Nura Auduga, bisa wannan tunani, inda yace “Mune ya kamata ace munyi wannan tunanin, to amma tunda ka ɗoramu a hanya to ina shamaka alwashin kafin karshen shekarar nan, zamu sake shirya irin wannan kuma zamu gayyaci manyan mutane daga ko ina a jihar Katsina don su shedi kokari da kwazon mutanen Safana, suma su koya.” inji Farfesa

A ƙarshe ya yi Nasiha ga ɗalibai da malamai akan ita gasa duk inda take akwai Nasara a cikinta, wanda  ma ake cewa ya fadi a gasar ba faduwa yayi ba Ilimi ya samu.

Alhaji Yahaya Barau wakilin Yariman Katsina, Nasiha yayi da yabo ga wannan hazikin ɗa nasu, wato Zulkifilu Nura. Sakataren Ilimi na garin Safana yayi ƙarin haske akan yanda Malami ya kamata ya kasance, da kuma yanda ya kamata ya zama ga ɗalibai.

Kwasa-kwasain da aka yi gasar a kansu sun hada da Harshen Turanci, Harshen Hausa, Ilimin Lissafi, Addinin Musulunci, da P.V.S

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here