Kungiyar 13×13 ta kama hanyar wargajewa?

0

Daga MUKHTAR YAKUBU.

@ katsina city news

Bisa ga dukkan alamu dai kungiyar mawaka ta 13×13 an zo wajen da za ta wargaje kowa ya kama gaban sa, a sakamakon ra’ayi na siyasa ko kuma son Kai na wasu daga cikin masu gudanar da harkokin kungiyar.

Tun farkon kafa kungiyar dai mutane sun sha mamakin haduwar mawakan da suka hadu suka hadu a cikin ta, saboda an tabbatar da ba a zama inuwa guda a tsakanin su Amma sai ga shi sun hadu a 13×13 Kuma kowa ya san a baya rigimar kudin kungiya ce ta sa aka rabu Kuma sai ga shi sun sake haduwa. Don haka a ke ganin tafiyar babu in da za ta je domin mai Hali ba ya fasa halin sa.

Instagram/13×13 movement
Instagram/13×13 movement

A farkon tafiyar 13×13 sun yi wani Salo na tara wa Kan su masoya tare da jawo hankalin mutane zuwa wajen su, ta yadda suka fito da salon bayar da gudummawa a gidajen yari da kuma raba jari ga matasa masu sana’a a Kan tituna don haka Jama’a suka rinqa kallon su a matsayin masu bayar da tallafi ga Jama’a.

Sai dai ga duk wanda ya koma jefe guda ya kalli 13×13 da kuma yadda take gudanar da tsarin ta. Zai fahimci kungiya ce ta ‘Yan maula mabarata’ yan jagaliyar siyasa, bambancin su da almajirai kawai da ba sa riqe kwano ko kuma su ce Allazi wahidin

Domin kuwa duk wani babban dan siyasa da ya fito neman shugaban kasa in ban da Atiku Abubakar kusan babu wanda ba su je sun yi maula a wajen sa ba.

Haka su ka rinka bin Gwamnoni suna ta yawon Allazi wahidin, idan an dawo a zauna a Hotel mai tsada a yi kasafin kudin Ha babba Ha karami.

Manufar tafiyar 13×13 manufa ce mai kyau a rubuce a takarda, Amma da aka zo tafiyar da ita sai ya zama an ajiye ta an Dora tafiyar a Kan wasu ‘Yan tsirsarun da in ba su suka fadi magana ba to ba za a dauka ba.

Baya ga haka duk wani mamba da aka samu yana da Alaka da Abdul Amat Shugaban YBN to hukuncin kora ta tabbata a Kan sa, don haka sai kungiyar ta koma adawa da Abdul Amat, tare da Bibiyar sa a Kan Abubuwan da yake gudanarwa.

 

13×13 ta zamo wata kungiyar da take ganin babu wanda ya Isa ya ja da ita, don haka ko da za ta kama Office ma sai ta je ta kama wani katon waje ta biya kudin haya na shekaru biyar. Kuma duk wanda ya ke Bibiyar Masana’antar Kannywwod babu wata kungiya in ban da MOPPAN da ta yi iya kaiwa shekaru 3 ba tare da ta wargaje ba, kai idan muka duba su kan su mawakan ba su taba kafa kungiyar da ta Kai shekaru biyu ba tun da aka kafa kannywwod.

A yanzu babbar barazanar da a ke ganin za ta wargaza 13×13 ita ce karya dokar kungiyar da wasu ke zargin Dauda Rarara ya yi na dakko tallar Tunubu shi kadai ba tare da sunan 13×13 ba, wanda a dokar ta za su yi tafiya daya ne kuka za a dakko Tallan dan takara ne da sunan 13×13.

Daman dai 13×13 hadin gambiza ne na wasu mawakan da kowa yana da Uban gidan sa na siyasa a wasu Jam’iyyu wanda ana ganin Tallan dan takara daya zai yi wahala ga 13×13, domin wasu daga cikin mawakan ba su taba yi wa APC ko Dan takarar ta waka ba. Shi ya sa a ke ganin daga an zo wannan zango kowa zai kama gaban sa.

Ko da tafiyar 13×13 ta wargaje a yanzu babu wanda ya ci gajiyar ta kamar Rarara, domin kafin kafuwar 13×13 tauraruwar sa ta yi kasa 13×13 ce ta dawo da saboda matsayin Shugabancin da ya rike, Amma mawaka da yawa an rufe su ne aka daina jin muryar su, wannan ya sa a yanzu da yawan su sun fara yin nadamar zaman su a cikin 13×13, domin sun gina wani ne sun rusa Kan su.

Muktar ya rubuto jaridun katsina city news daga Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here