IBRAHIM ZAKARI YA CHANZA SHEKA DA GA NNPP ZUWA SDP… Zai yi takarar gwamna a SDP

0

Mu’azu hassan

@ katsina city news

Alhaji Ibrahim zakari tsohon Mai taimakawa gwamnan katsina a fannin zuba jari.

Wanda ya Nemi jam iyyar NNPP ta tsayar dashi takarar gwamna a katsina.

Ya chanza sheka daga jam iyyar NNPP zuwa jam iyyar SDP..zakari yayi ta korafin rashin adalci da akayi masa a jam iyyar NNPP.inda har ya gudanar da taron Manema labarai akan haka. Ya kuma rubuta wasikun koke guda biyu ga uwar jam iyyar ta NNPP.

Uwar jam iyyar tayi zama akan korafin shi a farkon wannan satin .

Zakari ya bayyana cewa tunda ba zai iya samun adalci a jam iyyar NNPP ba, ya koma jam iyyar SDP wadda dama sun Dade suna zawarcin shi.

See also  Dan takarar jam’iyyar NNPP a Katsina ya bukaci a sake kirga kuri’u

Hedkwatar jam iyyar SDP ta kasa ta tabbatar ma da jaridun mu cewa. Ibrahim zakari shine Dan takarar gwamnan su a a jahar katsina.

SDP tsohuwar jam iyya ce, wadda marigayi shehu Musa yar adua ya kafa da abokan siyasar shi tun shekarar 1992.

Zakari matashi ne, Wanda ke shaawar siyasa,yayi aiki a gwamnatin APC,ya Nemi takara NNPP, yanzu kuma zai yi takara a jam iyyar SDP.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 .08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here