BINCIKE NA MUSAMMAN: WADANDA Suka Jagoranci Hari A Kan Tawagar Shugaban Kasa…… Sunayen su da Wanda ya kashe babban jami in yan sanda,

0

 

Mu’azu Hassan

 

@katsina city news

 

Jaridun Katsina City News, sun zurfafa bincike a kan su wa suka jagoranci hari a kan tawagar Shugaban Kasa a ranar Talatar da ta gabata?

 

Bincikenmu ya gano Daba biyar ta masu dauke da makami ce suka kai harin. Sun fito ne da niyyar satar dabbobi a yankin Safana da Dutsinma, kamar yadda majiyoyi daban-daban suka tabbatar mana.

Majiyarmu ta ce, Dankarami, gogaggen dan ta’addar nan da ke Yankin Zamfara shi ne ya zo da mahara masu yawan gaske a karkashin gayyatar Sani Muhiddinge, matashi dan shekaru 28, wanda yake daga Yankin Safana da Abu Radde daga Yankin Batsari da Sani Gurgu, da kuma Alhaji Abdul Karim.

 

Dukkanin su ban da Dankarami, sun taba tuba daga yin sata, kuma har gwamnatin Katsina ta rika hulda da su. Har ma suka rika shiga gaba ana ganawa da sauran barayin da ke rike da makamai a dazuzzukan Katsina.

 

Wadansu daga cikin su har sun taba dawo wa cikin gari da zama. Daga baya suka ta da tuban nasu suka koma ruwa tsundum.

 

Bincikenmu ya gano Dabar ’yan ta’adda hudu ce daga Jihar Katsina, kuma ta tsaffin tubabbu suka gayyato Dankarami daga Jihar Zamfara.

 

Majiyarmu ta tabbatar mana abin da ya kawo su, satar wasu shanu da ke Yankin Dutsinma a Jihar Katsina. Sun kuma yo gayyar ne domin dakile duk wata barazanar da za a iya masu wajen kwasar shanun, ko kuma barazanar jami’an tsaro, ko kuma ta ’yan’uwansu barayin da suke adawa da juna.

 

Majiyarmu ta ce Dankarami shi ne ya jagoranci maharan, saboda shi ne ya zo da yara masu yawa da kuma muggan makamai.

 

Sun zo da shirin yadda ake wa Dankarami kirari ne da Gwaska, su tafi da yawa, kuma cikin shirin ko-ta-kwana.

 

Majiyarmu ta tabbatar mana harin da aka kai wa tawagar Shugaban Kasa ba an yi ta ne bisa tsarin za a kai mata hari ba, ta fado ne a matsayin bazata.

 

“Lokacin da maharan suna kora shanunsu zuwa inda suka fito, sai suka ji jiniya, sai suka dauka sojoji ne suka kawo masu hari. Don haka sai su kuma suka kwanta masu.

 

“Suna matsowa inda suke sai suka bude masu wuta. Maharan a rediyo suka rika jin labarin cewa wadanda suka kai wa hari a garin Turare, tawagar Shugaban Kasa ce,” kamar yadda majiyoyi suka tabbatar mana.

Majiyarmu ta ce maharan sun ratsa garuruwa daban-daban a Kananan Hukumomin Safana, Dutsinma da Batsari, da wani Yankin Dan Musa, kafin su koma maboyarsu.

Wanda da an dau mataki mai kyau ana iya cimma masu da dakile su.

 

Garuruwan sune; Habul, Tawanka, Kunkunna, ’Yar Tandu, Koramar Saya-saya, Garhi, Turare da sauransu.

 

Mutanen yankun nan sun gan su suna tafiya cikin tawaga. Sun kuma gan su lokacin da suke dawowa da shanu da sauran dabbobin jama’a da suka sato.

 

Majiyarmu ta ce an so a samu matsala tsakanin Dankarami da wadanda suka gayyato shi, a kan rabon abin da aka sato.

 

Dankarami ya kwashe kusan kashi 80% na shanun, bisa hujjar cewa mutanensa sun fi yawa a cikin tawagar, kuma da makamai da dabararsa ta yaki aka yi amfani, kuma shi ne ya jagoranci harin.

 

Kuma da yake ya fi karfin su, dole suka kyale shi aka tafi da yadda ya tsara rabon dabbobin da aka sato.

 

Bincikenmu ya gano, a harin baki daya sun kashe sama da mutane 10, duk wanda ya kawo masu turjiya kisa ne, haka wanda ya yi masu rawar kai a kan hanya kisa ne, amma wanda ya gudu, ko ya zama dan kallo babu ruwansu da shi. Kamar yadda ganau suka tabbatar mana a garuruwan da maharan suka ratsa.

 

Binciken jaridunmu sun gano sunan dan ta’addar da ya kashe Area Commander Aminu Umar Dayi, sunansa Usman Modi Modi. Shi ke aiwatar da ta’addaci a yankin Kurfi da Dutsinma. Yana zaune ne a dajin Ummadau da Tsaskiya. Yana da mahara sosai. Shi ba ya cikin gamin-gambizar da ta kai wa tawagar Shugaban Kasa hari.

 

Amma a ranar Alhamis bayan tafiyar su Dankarami ya ba yaransa umurnin su shiga garuruwa su samo na Sallah, inda suka fita karkashin babban yaronsa, Alhaji Aibo. Kodayake jami’an tsaron yankin da hadin gwiwar ’yan banga sun dakile shirin nasu.

 

MATASHIYA

 

Jaridun Katsina City News, wadanda suka hada da jaridar Taskar Labarai da The Links News, sun goge a ba da labaran binciken musamman a Jihar Katsina da Arewa maso Yamma.

 

A 2014 jaridar Taskar Labarai ta ba da labarin cewa maharan dajin Rugu suna kara gogewar da gaba kadan za su fi karfin soja.

 

Sune suka fara bayyana sunan wanda ya jagoranci harin satar yaran makarantar Sakandire ta Kankara.

 

Sun ba da labarai da yawa a kan tsaro a Katsina da manya kafofin watsa labaran duniya irinsu New York times,Reuters da sauransu binciken da ya tabbatar da hakan.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here