Ta’aziyya: Hirata da Bishir Lawal Yar’adua, Mai Abin Mamaki.

0

 

Daga Danjuma Almizan

 

A tsakanin shekarun 2004 zuwa 2007, nakan raka Marigayi MD Yusufu a wasu tafiye – tafiye da ya kan yi.

 

Na sha ganin Yar’adua a manya Mayan Otel da mu kan sauka, a cikin nishadi da walwala da fira da jama’a.

 

A ban mantawa a Shekarar 2008 wata jarida ta san ya ni yi ma ta fira da shi, in har zai amince, a kan abin da ya shafi rayuwarsa, domin cike take da abubuwan ban mamaki.

 

Na same shi a gidan shi dake hanyar filin jirgi, na fada masa bukata ta, ta yin fira da shi, sai ya sake kallona, bayan ya yi dogon sai ya ce “in je in dawo”.

 

Haka na yi ta zarya, har gidan shi ya zamar man wajen Hira, wadda hakan ya yi man dadi, domin na karu da ilmoni da yawa, wadanda ba a samu a cikin litattafai, sai dai daga cikin irin mutanan dake zuwa wajen shi, da kuma abin da suke tattaunawa a gidan na shi.

 

Wani lokaci zai ce ma ni, zai yi tafiya, sai ya dawo in dawo, da haka har na shafe watanni hudu Ina zarya.

 

Wata asabar ban mantawa, da kanshi ya kira ni da safe, ya ce ” yanzu ya amince mu yi hira amma a kan wasan folo da kulob din shi na folo, amma kar a tabo rayuwar shi.

 

A kan haka mu ka yi hirar duk da haka sai da ya fadi wasu abubuwan da baya son a sa ni. Don haka Ina gida sai ga shi har gidana, ya ce “in dauko hirar nan ya sake jin ta, bai san na riga na sauke ta a email ba.

 

Na dauko, ya sake saurare, ya ce “yàwwa cire can, goge can”, aka dai sake wata hirar, muna gamawa ya kalle ni ya ce “Na sallame ka, amma duk lokacin da ka so kana iya zuwa zumunci, tunda na lura baka da karambani, ko shigar shugula”.

See also  FG empowers donkey farmers in Adamawa

 

Gaskiya ban Kara zuwa ba, sai dai a waya ko mun hadu a hanya, duk in da muka hadu, mukan dau lokaci, Ina daukar darasin rayuwa.

 

Wasu abubuwan da ya aikata, sun isa a sanya sunan shi a cikin kundin abubuwan ban Al’ajabi na Duniya, (Gunnies Book of Records).

 

misali ya taba hira da Jaridar New Nigeria a 1990, ya ce ” ya bai wa Mataimakin Shugaban Kasa na lokacin, cin hanci”. A kuma lokacin Babangida ne Shugaban Kasa, Agusta Aikome ne Mataimakin, ana buga hirar ya gudu zuwa Landan, sai da kura ta kwanta ya dawo, kuma ba abin da aka yi masa.

 

Yana da shekaru 27 a duniya, duk inda za shi da jirgin haya na kashin kansa ya ke yawo, yana dan shekaru 32 yana hulda da Shugabannin kasashe goma sha daya, a duniya. Ciki hare da Firaministan Burtaniya.

 

Yana da saukin Kai, amma kwalwar sa daban ce, yana da tausayin talakawa, duk wani dan karamin alhakin kwaro, babu ruwan shi da shi.

 

In ya yi dariya ya kada kafa, ko dai zai shirya tsiyar ko kuma an tuna baya.

 

Haduwa ta karshe da mu Kai da shi, a shekaru hudu da suka wuce, a legas, dai dai wajen hutawa na Otal din Chidex, Ina zaune sai na ji an ce, Nakatsina ikon Allah, yau kuma nan aka bullo?

 

Waya ta, ta karshe da shi da ya bugo man ya ce “zai yi takara a jam’6 PRP” a sani na, da shi yana da mata da ‘ya’ya. Haka kuma, duk tarayyar ku, kar ka yi masa maganar iyalan shi. Allah ya jikan sa da rahama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here