Sai dai gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakin dakatar da shi, an shirya tsaf domin nadin wani kasurgumin dan ta’adda, Ada Aleru, a matsayin Sarkin Fulani na Masarautar Yandoton Daji ranar Asabar Kamar Yadda Jaridar Premium Times Ta Ruwaito.
Wasu majiyoyi a gundumar da suka nemi a sakaya sunansu saboda dalilai na tsaro sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa an yanke shawarar mayar da ‘yan ta’addan a matsayin shugabansu ne da nufin samar da dawwamammen zaman lafiya a Masarautar Tsafe da ‘Yandoton Daji da ke fama da rikici da sauran yankunan Zamfara da Katsina. Jihohin da Mista Aleru da mukarrabansa ke kaiwa hari akai-akai.
Yandoton Daji na daya daga cikin sabbin masarautu guda biyu da gwamnatin Zamfara ta kafa a watan Mayu.
Matakin nada Mista Aleru a matsayin basarake ya biyo bayan tattaunawa tsakanin dattawan masarautar da Shugaban Yan Ta’addan.
Karin Bayani Na Nan Tafe.