Gwamnatin Zamfara ta Dakatar Da Sarkin Da Ya Naɗa Ɗan Ta’adda Sarauta

0

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Birnin ‘Yandoto, Aliyu Marafa bisa sarautar da ya baiwa dan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, wato Adame Aliero-Yankuzo wanda aka fi sani da da Ado Alero.

Matakin da masarautar ta ɗauka na naɗin sarautar ga dan ta’addan ya yi matukar shan kushe daga al’umma.

Saidai a jawabin da ya fito daga bakin sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Kabiru Balarabe, Fadar gwamnatin ta nesanta kanta daga sarautar da aka baiwa ɗan ta’addan, inda kuma bayan ta dakatar da Sarkin da ya bada sarautar, ta kuma kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here