Katsina United sun bamu Kunya…yakamata a sauke Shugabannin su. -Umar Isyaku Ogunse

0

Zaharaddeen Ishaq Abubakar

 

Umar Isyaku Ogunse Ciyaman na Talba Strikers yayi wannan kiran ne, da kakkausar Murya Duba da irin yanda Club ɗin na Katsina United da Official ɗinta suka tabka abin kunya (Suka kaimu Religation) duk da irin ƙoƙarin da mai girma Gwamnan Katsina Aminu Masari yake masu. Ogunse yace “Ina kira da Kakkausar Murya ga Gwamnan jihar Katsina da lallai ya duba lamarin Katsina United, kuma ya sauke dukkanin Shuwagabannin, saboda abin kunyar da suka jawoma jihar Katsina, jihar Shugaban ƙasa, du da ƙoƙarin Gwamna na faranta masu da basu dukkanin abinda ya dace domin suyi abinda ya kamata” Injishi

 

Ya kara da cewa Lallai wannan abin kunyar ba’ataɓa yinsa ba a tarihin jihar Katsina, sun kunyatar da ‘yan jihar Katsina, sun kunyatar da Gwamna sun kunyatar da Shugaba Buhari tunda jiharsa ce.

 

Yace; muna kirabga Maigirma Gwamna da a sauke su duka a sake zama, da Stockholders, domin sake Lale. Kowa ya san abinda ake a Katsina United sonkai ne da son zuciya. Yaja hankali.

 

A karshe ya bada shawara ga Maigirma Gwamna da ya sauke duk wani mai ruwa da tsaki a Katsina United, yayi Caretaker Committee kuma a kira Zaman gaggawa na Stockholders akan Ƙungiyar Kwallon kafa ta Katsina United.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here