Kampire ‘Jose’ Josefa, ‘yar shekara 28 ‘yar kasar Rwanda ba ta taba yin gashi a jikinta ba tun tana da shekaru biyar.
Kampire ta rasa duk gashinta ciki har da girarta bayan mutuwar mahaifinta bayan ya gama aske ta tana da shekara biyar.
Ba a cire gashinta gaba daya ba amma bayan sun gama zaman makoki ne ya fara zubewa a hankali. ‘Yan uwanta sun dauka an yi mata sihiri amma yanzu ba su san me za su ce game da lamarin ba.
Kanta ya koma Mai santsi tamkar madubi kamar bai taba gashi ba. Mahaifiyar Patricia da Kampire ta kai ta wurin likitan gargajiya a wani yunƙuri na gano abin da ke faruwa da ’yarsu. Ganye iri-iri ne aka mata wanda ta shafa a kai amma babu wanda ya yi aiki.
Lokacin da ƙoƙari na farko ya ci tura, sun nemi likita na gargajiya na daban amma babu wani canji.
“Mun gaji mun daina yin magani. An kashe duk ɗan kuɗin da muke da shi, ”in ji Patricia.
Ita ma Kampire ta rasa mahaifiyarta amma duk da haka ba su iya bayyana abin da ta mutu ba don haka ya jefa dangin cikin rudani.
Bayan mahaifiyarta ta rasu, kafafun Kampire sun fara samun matsala kuma ta zama Mai tawaya Wato nakasa.
“Kafa ɗaya ta fara lanƙwashewa da kanta. Har yanzu yarinya ce kuma muna mamakin menene ke damunta,” in ji Patricia.
A wannan lokacin suka yanke shawarar kai ta asibiti kuma wannan lokacin magani ya yi aiki.
Bayan haka, suna jira su ga ko gashinta zai girma, amma ba abin da ya faru har ta girma. Kampire ya yi aure amma aurenta bai daɗe ba tunda abokan mijinta suna yi masa ba’a suna yi masa ba’a saboda irin matar da yake da ita.
“Na shafe watanni 6 tare da mijina amma abokansa sun ci gaba da yi masa dariya saboda ni sai muka rabu,” in ji Kampire.
Waɗannan abokanan sun ba shi shawarar ya rabu da ita domin da alama ‘ya’yansu ne za su gaji halin da take ciki.
Bayan aurenta ya mutu, Kampire ta koma gidan kakarta. Ta sha alwashin ba za ta kara aure ba.
“ba zan kara aure ba, bata lokaci ne, ba zai taba alfahari da ni a matsayina na matar sa ba.”