‘Yan ta’adda sun kashe mutum 6 tare da raunata wasu a jahar Katsina

0

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da harin da ‘yan ta’adda suka kai cikin dare wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 tare da jikkata wasu 6 a karamar hukumar Faskari da ke jihar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Sufeto Gambo Isah wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an kai harin ne a kauyen Ruwan-godiya.

 

A cewar Isah, ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 1:30 na yammacin ranar Talata inda suka kashe mutane shida yayin da wasu shida suka jikkata.

 

Ya kara da cewa, an kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitoci domin yi musu magani yayin da ‘yan sanda ke a Garin domin tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya a yanki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here