Ƙidayar Gwaji a Daura: Kwamishina Banye yayi Rangadi a shiyoyi 6 Don ganin yanda Aikin ke gudana…

0

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

 

Da safiyar ranar Alhamis 21 ga watan Yuli Kwamishinan ƙidayar Jama’a na ƙasa Shiyyar jihar Katsina, Injiniya Bala Almu Banye da tawagar sa, suka ratsa shiyoyi shida na garin Daura, domin gani da Ji daga bakin ma’aikatan da mutanen gari irin yanda Aikin ke gudana.

 

Injiniya Banye ya Saurari ƙorafi da kuma irin nasarorin da ƙidayar ta Gwaji ta samu, a inda ma’aikatan suka tabbatar da aikin ƙidayar yana gudana yanda ya kamata  gami da samun haɗin kan al’umma.

A ƙidayar ta Gwaji, Injiniya ya tambaye su, yanayin inganci da saurin aiki na Na’ura da suke amfani da ita, inda suka tabbatar da aikin na tafiya yanda ya kamata, saidai a Unguwar da ake kira, Bakin Asibiti. Duba da yanki ne mai yawan Al’uma da shiyyoyi daban-daban jami’an sun gabatar da ƙorafinsu akan bazasu iya kammala aikin a cikin ‘yan kwanakin da aka ɗibar masu ba.

 

Inda Kwamishina Banye a take ya sanar da Babban Ofishin ƙidaya dake Abuja Babban Birnin tarayya domin duba yiyuwar ƙara masu kwanika.

 

Injiniya yayi tsokaci ga manema labarai akan irin yanda tsarin, ƙidayar yake. Sana kuma yayi ƙarin haske, akan masu cewa Ansanya addini ko ɓangaren wata aƙida acikin jerin tambayoyin da akewa mutane. Yace “wannan zancen ƙirƙirane baya cikin tsarin tambayoyin da akewa mutane”

 

“Muna gudanar da Aikin mu ba tare da sanin ko tambayar kai kirista bane, ko Musulmi, Ɗan’izala ne kai, ko ɗan ɗariƙa, duk tambayoyin mu basu shafi wannan ba” inji Banye.

Zarman na Katsina, kuma Kwamishinan ƙidayar na ƙasa, a shiyyar Katsina Injiniya Bala Almu Banye ya tabbatar da cewa har yanzu basu fara ɗaukar ma’aikatan da zasu yi Aikin ƙidayar na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku ba. Saɓanin abinda ke yawo a Kafafen sada zumunta cewa; sun ɗauki ma’aikata, yace wannan ba gaskiya bane “Idan amfara ɗauka kowa zai sani, kuma muna sa ran ɗaukar ma’aikatan ƙidayar guda Miliyan ɗaya, sana a yanar gizo ne zamu buɗe inda duk mai buƙata zai cike Fom da duk ƙa’idojin da muke nema na Ilimi, sana daga shekara goma sha takwas ne abinda yayi gaba idan mutum bai kai waɗannan shekarun ba ba zamu ɗauke shi, ba kuma da zamuyi amfani da (National Identification number NIN) wato katin zamanka ɗan ƙasa.) Banye ya tabbatar.

See also  Kai Tsaye: Sakamakon Zaben Gwamna Daga Kananan Hukumomin Jihar Katsina

 

Yankunan da Kwamishinan ya ziyarta sun haɗa da Makara-Huta, Kalgo, Tawalala, (Bakin Asibiti) Wala, (Asibitin Dabbobi) (Veritinary Clinic) Duk acikin ƙaramar Hukumar Daura a jihar Katsina.

 

A shekara ta dubu biyu da Ashirin da uku ne za’ayi ƙidaya ta ƙasa a duk faɗin Najeriya, domin haɓaka da raba tattalin arziki ƙasa bisa ƙa’ida domin cigaban ƙasa inda a yanzu ake gudanar da ƙidayar Gwaji, duba da irin dogon lokaci da aka ɗauka ba tare da anyi ƙidayar ba, kuma da yanda aka zamanantar da aikin na ƙidaya wato (Digital) yana buƙatar Gwaji kafin fara ƙidayar gadan-gadan.

 

Domin ganin Shirin yanda Aikin ƙidayar ya kasance ku je a Playstor ku sauke Manhajar Katsina City News zaku ga dukkanin Shirye-shiryen mu na Radio ? da Talabijin ? da karanta Labarun mu kai tsaye a yanar gizo, fa sauran Kafafen mu na sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here