DA DUMI-DUMIN SA: Yan Bindiga Sun Kashe Dan Majalisar Adamawa

0

Mataimakin shugaban majalisar dokokin karamar hukumar Song, Hon. Ishaya Babakano Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Ishaya Babakano a jihar Adamawa.

 

An kashe Babakano ne a daren Juma’a a gidansa da ke unguwar Gudu Mboi a karamar hukumar Song.

 

An bayyana cewa an harbe kansilan har lahira sa’o’i kadan bayan da maharan suka yi garkuwa da shi a garinsa na Bannga.

 

Har ila yau, an ce an harbe dansa a cikin lamarin kuma an ce yana karbar magani a wata cibiyar lafiya da ke Song.

 

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, don haka ta tura jami’anta domin gudanar da bincike kan harin da nufin kamo masu laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here